Birtaniya

An yi gangamin addinai a Birtaniya

Gangamin zaman lafiya tsakanin musulmi da Kirista da Yahudawa a London
Gangamin zaman lafiya tsakanin musulmi da Kirista da Yahudawa a London AFP via Yahoo

Mabiya addinan Islama da Kirista da Yahudawa, sun gudanar da wani taron gangami a birnin London na Britaniya, domin neman hadin kai tsakanin addinan. Ma su gangamin sun bayyana cewa ‘yan ta’adda, ba za su haifar da rarrabuwan kai ba a tsakaninsu ba.

Talla

Gangamin mataki ne na nuna adawa da hare haren da aka kai a Faransa da Denmark.

Rahotanni sun ce sama da mutane 100 ne da suka hada da shugabannin addini a Birtaniya da kananan yara suka shiga gangamin da aka gudanar a ranar Alhamis.

Gangamin na zuwa ne a yayin da ‘Yan sandan Birtaniya suka cafke wani matashi da ake zargi yana shirin kai hari.

‘Yan sandan sun cafke matashin ne mai suna Brusthom Ziamani dan shekaru 19 yana rike da wuka da guduma tare da tutar Mayakan IS da ke da’awar Jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.