Faransa

Kamfanin Areva zai kori ma’aikata 1,500 a Jamus

Ginin Kamfanin Areva a Faransa.
Ginin Kamfanin Areva a Faransa. Reuters

Kamfanin Areva da ya shahara wajen hako makamashin Uranium a duniya, ya sanar da sallamar ma’aikatansa 1,500 a reshensa da ke kasar Jamus. Mai magana da yawun kamfanin ya ce za a kammala sallamar ma’aikatan ne kafin karshen shekara ta 2017 sakamakon matsaloli na rashin kudi da suke fuskanta.

Talla

A Kasar Jamus kawai kamfanin Areva na Faransa na da cikakkun ma’aikata da yawansu ya haura dubu biyar. Kuma kungiyoyi kwadago na fargaba akan yiyuwar kamfanin zai rufe cibiyoyinsa 8 a kasar.

Tuni Kamfanin ya ce ya yi hasarar makudan kudi, kuma rage yawan ma’aikatansa na daga cikin matakan da zai dauka domin farfado da darajarsa.

Kamfanin ya ce ya yi hasarar Euro milyan dubu da 800 a shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.