Kungiyar Tarayyar Turai

Hatsuran Mota a bara sun kashe Mutane Sama da dubu 24 a Turai

Wani hatsarin mota
Wani hatsarin mota Tristan Savatier/Getty Images

Wani rahoto da kungiyar tarayyar Turai ta fitar ya ce, sama da mutane dubu 24 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsurran mota a cikin shekarar bara a yankin na Turai kawai  

Talla

Kwamishinar da ke kula da harkokin sufuri na kungiyar, Violeta Bulc, ta ce dole ne kasashen yankin, su kara daukar sabbin matakai domin rage faruwar hatsurra kan titunansu lura da yadda suke faruwa fiye da yadda aka yi hasashe.

Nanda shekara ta 2020, Kungiyar Tarayyan Turan, ke sa ran raguwar aukuwar hatsura da kusan rabi na alkaluman da ake samu a yanzu.

A shekara ta 2010 kadai, kimanin mutane dubu 31 ne suka rasa rayukansu a turan sakamakon hatsuran mota.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.