Libya-Turai

An ceto ‘yan gudun hijita 300 a gabar Ruwan Kogin Mediterranean

Migrants standing on the vessel Ezadeen at Corigliano Calabro harbor in southern Italy, 3 January  2015.
Migrants standing on the vessel Ezadeen at Corigliano Calabro harbor in southern Italy, 3 January 2015. Reuters/Antonino Condorelli

Dakarun Sojin Ruwan Tekun Atlantika masu sintiri a gabar Ruwan Kogin Mediterranean sun ceto fiye da ‘yan gudun hijira 318 tsakanin gabar Ruwan Cicily da kasar Libya, a wani bangare na aikin sintirin da suke na gadin yankunan kan iyakokin kasashen nahiyar Turai

Talla

Wata kafar watsa labarai ta kasar italiya ta ruwaito cewar makeken jirgin ruwan da ke dauke da ‘yan gudun hijirar ya isa a gabar Ruwan Cicily na yankin Pozzallo ne da marecen jiya dauke da ‘yan gudun hijirar da aka ceto ciki kuwa, hadda kananan yara 14 da kuma mata 5 masu tsohon Ciki, wadanda daga bisani aka yi gaggawar kaisu Assibiti.

Haka ma ‘yan sandan kasar Italiya sun bayyana kama mutane 8 ‘yan kasar Tunisia da ake zarginsu da safarra bil’adama.

Rahoton kafar watsa labarain ya ce ‘yan gudun hijrar da aka ceto, gamin gambizar mutane daga kassahe 13 ne da suka hada da Sudan da Ghana da Morocco da Mali da Mauritaniya da Senegal da Pakistan, da Najeriya da Syria da palesdinu da Eritria da Indiya da kuma kasar Tunisia, suna kokarin tsallakawa Turai ta barauniyar Hanya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.