Isa ga babban shafi
Faransa

An kai wa tashar TV5 harin intanet

Ministocin faransa dake ziyara a gidan talabijin TV5
Ministocin faransa dake ziyara a gidan talabijin TV5 REUTERS/Benoit Tessier
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 2

Tashar TV5Monde a Faransa da ke watsa shirye-shiryenta a cikin yaren Faransanci a kasashe sama da 200 na duniya, ta fuskanci hari daga masu kusten shafukan Intanet kuma ana zargin kungiyar ISIL ne da ke ikirarin jahadin islama a duniya.

Talla

Ba a tantance yadda maharan suka kai harin ba, kwarraru da ke bicinke a kai sun bayyana cewa, sun kai harin ne ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa na gidan talabijin.

A zantawarsa da gidan Radiyo Faransa shugaban gidan Talabijin na tv5 Yves Bigot ,ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko, a tarihi da aka taba samu hari ta hanyar yin amfani da hanyoyin sadarwa na zamani zuwa wani gidan talabijin.

Sa’o’i bayan kai harin a ranar Laraba, wasu da ke ikirarin cewa 'yan kungiyar ISIL ne sun dau alhakin harin.

Tuni dai Gwamnatin Faransa ta aika da ministan cikin gida Bernard Cazeuneuve tare da rakiyar ministan sadarwa da na al’adu Fleur Pellerin da kuma ministan harakokin waje Laurent Fabius, zuwa gidan talabijen tv5 domin nuna alhinin Gwamnatin kasar  tare da bayar da goyan baya zuwa ga Shugabanin tashar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.