Ukraine

An cafke mutane 39 da ke shirin bore a Ukraine

Masu zanga-zanga a Ukraine
Masu zanga-zanga a Ukraine REUTERS/Maxim Shemetov

Hukumomin Ukraine sun ce sun kama wasu mutane 39 da ke shirin kaddamar da bore dan goyan bayan ‘Yan Tawayen kasar da ke samun goyon bayan Rasha a Odessa kudancin kasar. Sanarwar na zuwa ne a lokacin da shugaba Petro Poreshenko ke shirin tafiya bikin cika shekaru 71 da sojojin Rasha suka ‘yantar da Yankin daga hannun ‘Yan Nazi.

Talla

Hukumar leken asirin Ukraine sun ce sun kuma kwace tarin makamai daga hannun wadanda aka kama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.