Italiya

An ceto bakin haure 1,000 a tekun Italiya

Bakin Haure da ke kokarin shiga Turai
Bakin Haure da ke kokarin shiga Turai REUTERS/Antonio Parrinello

Hukumomin Kasar Italiya sun sanar da ceto bakin haure kusan 1,000 daga cikin teku kusa da gabar ruwan kasar Libya. Jami’an da ke gadin gabar ruwan sun ce bakin hauren sun aike da sakon neman dauki ne lokacin da kwale-kwalen da suke ciki ya fuskanci igiyar ruwa, abinda ya sa aka kai musu taimakon gaggawa.

Talla

Jami’an ruwan na Italiya sun kuma yi nasarar kubutar da wani kwale kwale mai dauke da mutane 73, wadanda aka bayyana ‘yan Syria ne da Kurdawa da ‘Yan Somalia da ke kokarin tsallakawa zuwa Turai.

Akalla mutane 480 aka tabbatar da mutuwarsu cikin watanni uku a bana wadanda ke kokarin shiga Turai.

A shekarar da ta gabata baki 3,500 daga Afirka da Gabas ta Tsakiya suka mutu a kokarin tsallakawa zuwa Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.