Fadar Vatican-Turkiyya
Turkiyya ta gayyaci jakadan fadar Vatica kan kisan kiyashi aka yiwa Armeniyawa
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kasar Turkiyya ta gayyaci jakadan fadar Fafaroma ta Vatican dake kasar, domin yayi mata bayani kan manufar kalaman fafaroma Francis dake ikirarin kisan kiyashi aka yiwa Armeniyawa, a hannun dakarun Othman lokacin yakin duniya na farko.Babu dai bayanai gameda abubuwan da ake bukatar sani daga jakadan amma kuma ma’aikatar harkokin wajen Turkiyyan na cewa nan gaba za a fitar da sanarwa kan lamarin.Kasar Turkiyya tasha nuna rashin amincewa da kalaman kisan kiyashi, da aka yiwa Armeniyawa a yakin duniya na farko.