Turai

Amnesty ta soki Turai akan batun bakin haure

Bakin Haure da ke kokarin shiga Turai
Bakin Haure da ke kokarin shiga Turai REUTERS/Guglielmo Mangiapane

Kungiyoyin kare Hakkin Bil Adama a kasashen Turai sun yi allawadai da matakin da hukumomin kasashen da ke Yankin suka dauka na kawar da kansu ga aikin ceto daruruwan bakin hauren da suka mutu a cikin teku. Matakin na zuwa ne sakamakon rahotan mutuwar bakin haure 400 a teku wadanda ke neman tsallakawa Turai don samu rayuwa mai inganci.

Talla

Kungiyar Amnesty International ta ce sakacin kasashen Turan shi ke haifar da mace macen da ake samu yanzu haka.

Daraktan kungiyar Gauri van Gulik, ya ce bai san adadin mutanen da kasahsen Turai ke bukatar ganin sun mutu ba kafin su dauki mataki a kan matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.