Birtaniya

Mutane Miliyan biyu sun yanki rijistar zaben Birtaniya

Firaministan Birtaniya David Cameron
Firaministan Birtaniya David Cameron REUTERS/Peter Macdiarmid

Mutane sama da miliyan biyu ne suka yi rajistar zaben da za a yi a Birtaniya yayin da wa’adin rajistar ya cika daren jiya. Hukumar zaben kasar tace daga cikin wadanda suka yi rajistar miliyan daya da dubu dari tara sun yi rajistar ne ta waya, yayin da sauran suka je ofishin hukumar zabe.

Talla

Kididdigar da hukumar ta fitar ya nuna cewar 570,000 daga cikinsu na tsakanin shekaru 16 zuwa 24.

A tsarin Birtaniya ana yin rajista tun mutun na shekara 16 amma kuma ba a yin zabe sai an kai shekara 18.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.