Birtaniya

Tattalin arzikin Birtaniya na tafiyar hawainiya

David Cameron na Birtaniya
David Cameron na Birtaniya REUTERS/Stefan Wermuth

Tattalin arzikin britaniya na tafiyar hawainiya wajen samun habbaka a cikin watanni hudu na farkon shekarar 2015, kasa da yadda masu hasashe ke tsammani, kamar yadda hukumomin kasar suka sanar, al’amarin da a yanzu ke barazana ga gwamnatin kasar, a dai-dai lokaci da ya rage kwanaki 9 a gudanar da zabe a kasar.

Talla

Yawan kayayyakin da kasar ke samarwa ya habbaka ne da maki 3 cikin dari daga watan janairu zuwa maris, sabanin bara da ake da digo 6 cikin 100.

Firaministan kasar David Cameron yace wannan na nuna cewa, akwai bukatar mayar da hankali akan shirin gwamnatin kasar na tattalin arziki domin samar da ci gaba a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.