Italiya

Italiya ta jaddada kiranta ga EU kan kwararar bakin haure

Jirgin ruwa dauke da dimbin bakin haure a Tekun Mediterranean
Jirgin ruwa dauke da dimbin bakin haure a Tekun Mediterranean REUTERS/Ismail Zitouny

Hukumomin Kasar Italiya sun jaddada kiransu ga Kungiyar kasasashen Turai da ta taimaka wajan magance matsalar kwararar bakin haure zuwa nahiyar Turai

Talla

Wannan na zuwa bayan nitsewar wani kwale- kwale a gabar ruwan tekun Italiya, inda mutane 40 suka rasa rayukansu.

Hatsarin ya auku ne sakamamkon fashewar inji yayin da 137 daga cikinsu suka tsira kuma sun tabbatar da cewar, da dama daga cikinsu sun rasa rayukansu sabanin yadda aka ce 40 kacal ne suka mutu a hatsarin.

Hukumimin kasar na Italiya sun ce, suna sa ran bakin haurre da dama zasu shigo kudancin Kasar daga nan zuwa watan Satumba mai zuwa, yayin da a bara aka samu kimanin bakin haure dubu 170 da suka shigo kasar.

A dayan bangaren kuwa, ministan harkokin wajan Italiya Paolo Gentiloni ya bayyana cewar ya kamata kungiyar kasasshen turai ta taimaka wajan yaki da masu safarar bakin haure kuma ta samar da tsare tsare dangane da baiwa bakin haure mafaka.

Kawo yanzu dai kimanin bakin haure 1,750 ne suka hallaka a tsakanin gabar ruwan Libya dana Italiya tun a farkon shekarar nan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI