Faransa

Faransa ta karfafa aikin leken asiri

Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande
Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande Reuters

Majalisar Kasar Faransa ta amince da shirin bai wa jami’an tsaron kasar karin karfin gudanar da bincike da kuma liken asiri kan mutanen da ake zargin duk da sukar kungiyoyin kare hakkin bil Adama ke yi. ‘Yan Majalisun wakilai 438 suka amince da dokar yayin da 86 suka ki amincewa da ita.

Talla

Yanzu za a kai dokar majalisar Dattawa don samun goyan bayanta.

Kungiyar Amnesty International ta soki dokar wadda ta ke cewar za ta mayar da Faransa zama kasar da ke sa ido kan al’ummarta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.