Faransa

Malaman Makaranta na yajin aiki a Faransa

Shugaban Faransa François Hollande
Shugaban Faransa François Hollande REUTERS/Alain Jocard

Malaman makaranta a Faransa na gudanar da yajin aiki domin nuna adawa da sauye-sauyen da gwmanatin kasar ke neman aiwatarwa a bangaren makarantun Sakandare na kasar. Ministan ma’ikatar ilmin kasar Najat Vallud-BelKacim, na fuskantar suka daga malamai da iyayen yara sakamakon wadannan sauye-sauye, yayin da jam’iyyun adawa ke neman yin amfani da batun wajen kalubalantar gwamanati.

Talla

Wasu daga cikin sauye-sauyen da ma’aikatar ilimin ke neman aiwatarwa sun hada da soke wasu darussa da kuma karawa makarantun damar daukar dawainiyar kansu a maimakon gwamnati.

Belkacem ta soma aiwatar da wadannan sauye-sauye ne domin samar da daidaito ta fannin ilimi tsakanin ‘yayan attajirai da kuma masu karamin karfi.

A wani rahoto da ta fitar a baya, wata kungiya mai suna OECD, da ke sa ido kan ci gaban da ake samu a kasashen duniya, ta ce Faransa na daya daga cikin kasashe da ake da bambanci ta fannin samar da ilimi a tsakanin rukunin al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.