Faransa

An kamala bikin nuna fina-finai na cannes a Faransa

REUTERS/Regis Duvignau

An kamala bikin nuna fina-finai na Cannes a kasar Faransa karo na 63 a duniya,Bikin dai ya samu halartar mayan masu tsara fina-finai na Duniya dama Gwamnatocin kasashe.Taron dai ya samu hallatar fitattun masu tsara fina-fanai daga sassa dabam-dabam na Duniya.

Talla

A wannan karon dai ‘yan faransa ne suka samu nasara lashe kyaututuka da dama, kama daga wanda ya tsara fim din daya fi ko wane tasiri a duniya.

Jacques Audiard mai shekaru 63 na daya daga cikin mutane da suka samu kyauta da ta fi kowace a wanan taron da ake kira Palme D’or.
Jacques dai ya bayana matukar farin cikin sa tare da nuna yabawa ga daukaci wadanda suka taimaka masa wajen samun wannan nasara.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya bayyana goyan bayan sa, ga duk wani tsari da masu tsara fina finai ke bukata a kasar, domin samar da cigaba a harkokin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.