HSBC: Dakta Kasim Kurfi

Sauti 03:44
Kasimu Garba Kurfi
Kasimu Garba Kurfi APT SECURITIES

Bankin HSBC daya daga cikin manyan bankunan duniya, ya sanar da matakin korar ma’aikatansa kimanin 50,000 tare da rufe cibiyoyinsa a Brazil da Turkiya da kuma dauke babban hedikwatarsa daga Birtaniya zuwa kudancin China. Matakin na zuwa ne a yayin kasashen duniya ke ci gaba da sa wa Bankin ido kan yadda attajiran duniya ke boye kudi don kaucewa biyan haraji. Awwal Janyau ya tattauna da Dr Kasim Kurfi shugaban Kamfanin APT da ke hada-hadar hannayen jari a Najeriya.