Georgia-Yanayi

Ambaliyar Ruwan sama ta yi sanadiyar mutuwar mutane 12 a Jojiya

yanzu haka dai masu kula da namun daji na ci gaba da farautar namun daji a tsakkiyar birnin Tbilissi na kasar Jojiya, bayan da ambaliyar Ruwan sama da aka sheka a birnin ta rusa gidan namun dajin da a halin yanzu suka fantsama a cikin gari

Wata Dorina a kan titin birnin Tbilissi na kasar Georgia , a ranar  14 Yuni 2015.
Wata Dorina a kan titin birnin Tbilissi na kasar Georgia , a ranar 14 Yuni 2015. REUTERS/Beso Gulashvili
Talla

A kalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu a yayinda wasu da dama suka bata, sakamakon wata ambaliyar ruwan sama da ta mamaye Tibilisi babban birnin kasar Georgia, tare da lalata wani gidan namun daji, al’amarin da yayi sanadiyar fantsamar zakoka, damusa Dorinai da kadoji a kan titunan birnin.

Mahukumtan kasar sun bukaci al’amma su zauna a cikin gidajensu su kuma kulle kafin shawo kan matsalar.

Yanzu haka dai kimanin karnukan dawa 20 da zakoka 8 tare da fararen Damisa, Dila suka kasance ko dai sun bat aba a san inda suke ba ko kuma rundunar dake kula da ayuka na musaman sun harbesu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI