Georgia

Ana farautar Damisa da ta tsere a gidan zoo a Georgia

Damisar Daji
Damisar Daji DR

‘Yan sandan kasar Georgia sun kaddamar da farautar wata Damisa da ta tsere a gidan da ake ajiye damun dajin a Tbilisi bayan wata Damisar ta kashe mutum kafin a samu nasarar kashe ta.

Talla

Hukumomi a birnin Tiblisi sun bukaci jama’a da su yi hattara domin kuwa har yanzu akwai sauran dabbobin daji da ke ci gaba da gararamba a cikin birnin, bayan da ambaliyar ruwa ta fasa inda ake tsare da wadannan dabbobi a farkon wannan mako.

A jimilce dai an bayyana cewa akwai dabbobi da suka hada da Dakuna da Damisa da Kadoji, da sauransu, akalla 600 wadanda ake tsare da su a cikin gidan ajiye dabbobin dajin kafin ruwa ya yi awon gaba da su.

Mai magana da yawun hukumar adana dabbobin daji na kasar Mzia Shara-shidze, ya ce kawo yanzu an kama, tare da sake dawo da mafi yawan dabbobin, amma kuma akwai alamun da ke tabbatar da cewa har yanzu ba a gano sauransu ba.

Wani ruwan sama mai karfin da aka yi a birnin na Tbilisi, ya haddasa mummunar barna tare da ruguza gidan da ake tsare da dabbobin, inda har aka samu hasarar rayukan mutane 19 cikinsu kuwa har da ma’aikatan da ke kula da dabbobi su 3.

Daga bisani dai wata Damisa da ta tsere sakamakon fasa wurin da ake tsare da ita, ta kai hari tare da kashe

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI