Faransa

Ministan wajen Faransa na ziyara a Gabas ta Tsakiya

Ministan harkokijn wajen Faransa, Laurent Fabius
Ministan harkokijn wajen Faransa, Laurent Fabius AFP PHOTO / KENZO TRIBOUILLARD

A yau asabar ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya fara ziyarar aiki a wasu kasashen yankin gabasr ta tsakiya a yunkurin farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasdinu.

Talla

Fabius zai ziyarci kasashen Masar, Jordan, yankin Palasdinu da kuma Isra’ila. Faransa dai na fatar ganin an mayar da wannan tattaunawa ta zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu a karkashin inuwar wani gundun kasashe.

Hari la yau Faransa na fatar ganin an samar da wani sabon kuduri na Majalisar Dinkin Duniya da zai goyi samar da dawwamammen zaman lafiya da kuma ‘yantacciyar Palasdinu a karkashin iyayokin shekarar 1967.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.