Bosnia

Bosnia na bikin cika shekaru 20 da jimamin kisan Musulman Kasar

Dubban masu Macin tunawa da kisan kiyashin
Dubban masu Macin tunawa da kisan kiyashin (Photo : Reuters)

Dubban mutanen Bosnia sun soma bikin cika shekaru 20 da jimamin kisan kiyashin da aka yi wa Musulman kasar a birnin Srebrenica inda aka kashe mutane sama da dubu 100.

Talla

Dubban mutane ne suka fara tafiyar nisan kilomita 100 domin juyayin kisan kiyashin.

An soma bikin jimamin ne saura kwanaki uku a cika shekaru 20 da kisan kiyashin da aka yi musulman na Bosnia.

Dubban mutanen da ke macin su nufi gabashin Srebrenica domin bin sawun musulman Bosnia da suka nemi tsira daga dakarun Serbia a lokacin yakin.

Majalisr Dinkin Duniya ta ce adadin musulman Bosnia 10,000 zuwa dubu 15 suka taka da kafa a yayin da suke gudun tsira a shekara ta 1995.

An kiyasta Adadin mutane 8,000 da aka kama ko aka kashe bayan faduwar birnin Srebrenica.

Akwai makeken kabari da aka gano shake da gawarwakin musulman Bosnia sama da 6000 a shekara ta 2006.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane sama da dubu dari aka kashe a yakin Bosnia tsakanin shekara ta 1992 zuwa 1995.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.