Italiya

Kwale-kwale ya kife da daruruwan ‘Yan ci-rani a teku

Daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu bayan da wani kwale-kwalen kamun kifi da ke dankare da daruruwan ‘yan ci-rani ya nutse a tsakiyar Teku, gabar ruwan Libya a jiya Laraba.

Ana kokarin ceto 'Yan ci-raini a tekun Italiya
Ana kokarin ceto 'Yan ci-raini a tekun Italiya REUTERS/Marta Soszynska/MSF
Talla

Kungiyar da ke kula da tafiye-tafiye ta duniya (OIM) ta ce kiyasta cewa sama da mutane dubu biyu ne suka rasa rayukansu a bana a tekun Méditerranéen.

Kuma nutsewar da kwale-kwalen ya yi a jiya Laraba, ana ganin zai iya kasancewa hatsari mafi muni tun bayan wanda ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan ci-raini 800 a watan Afrilun da ya gabata a tekun.

Kakakin hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Italiya Federico Fossi, ya ce jirgin wanda ya nutse a jiya laraba na dauke ne da bakin haure sama da 600, amma an ceto 250 daga cikinsu.

Hukumomin Italiya sun ce mutaneu 16 suka rasa rayukansu a hatsarin kwale-kwalen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI