EU

EU ta soki kasashen Turai akan matsalar bakin haure

Dubban 'Yan ci rani ne ke kokarin bi ta mashigin Calais daga Faransa domin shiga Birtaniya
Dubban 'Yan ci rani ne ke kokarin bi ta mashigin Calais daga Faransa domin shiga Birtaniya REUTERS/Pascal Rossignol

Hukumar Kungiyar kasashen Turai ta soki jinkirin aiwatar da tsare-tsaren kasashen da ke haifar da hasarar rayukan bakin haure da ake samu kusan a kullum, wadanda ke kokarin tsallakawa zuwa kasashen.

Talla

A cikin wata sanarwan hadin guiwa da suka sanya hannu, Frans Timmermans mataimakin Shugaba na farko, na Hukumar kungiyar kasashen Turai, da Federica Mogherini shugaban harkokin waje na kungiyar, da kuma Kwamishinan kula da bakin haure na kungiyar Dimitris Avrampoulos, na cewa akwai bukatar a rika aiwatar da dukkan kudirori da aka zartas.

Kalaman nasu na zuwa ne sakamakon rasa rayukan bakin haure kusan 200 a tekun Bahrun bayan sun bar gaban ruwan Libya cikin wani kwale-kwale a shekaranjiya.

Kwale-kwalen na dauke da mutane sama da 600 a lokacin da ya sami tangarda yana tsakiyar teku.

A bana kawai jimillan mutane sama da 2,000 suka rasa rayukansu, wasu kusan dubu 190 aka kubutar da su daga salwancewa a teku, akan hanyarsu ta zuwa ci-rani a Turai.

A watanni hudu da suka gabata Bayan mummunar hasarar rayukan ‘yan ci-rani 800 da aka samu, shugabannin kasashen Turai 28 sun tsaida shawarar daukan matakan gaggawa don kawo karshen matsalar, ciki har da shawaran amfani da sojan ruwa domin kama masu safarar bakin hauren da ke Libya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.