Girka

Girka ta kulla yarjejeniyar karbo rance na Euro biliyan 85

Firaiyi Minista  Girka Alexis Tsipras
Firaiyi Minista Girka Alexis Tsipras

Gwamanatin Kasar Girka ta sanar da cewar tayi nasarar kulla yarjejeniyar karbar rancen kudin da suka kai euro biliyan 85 daga masu bata tallafi na kasashen duniya dan ceto tattalin arzikin kasar da ya tabarbare.

Talla

Ita ma kungiyar kasashen Turai tace wakilan ta sun kulla yarjejeniya ta wucin gadi da hukumomin na Girka, wanda itace ta uku tun shekarar 2010.

Kwamishiniyar kudin kungiyar Annika Breidthardt tace abinda suke jira kawai shine amincewar bangaren siyasa daga shugabanin kasashen su.

Hakazalika a yau talata Asusun Lamuni na duniya da kuma Bankin Turai sun amince da bai wa kasar Girka kashi na uku na basusuka domin tayar da komadar tattalin arzikinta.

A karkashin wannan shiri dai, cibiyoyin za su zuba wa Girka kudaden da yawansu ya kai Euro bilyan 85 a cikin shekaru uku masu zuwa, kuma za a bai wa kasar bilyan 10 a cikin gaggawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.