Faransa

Masu yawan bude ido na wannan shekarar zasu yawaita a Faransa

Masu Yawan bude ido a Faransa
Masu Yawan bude ido a Faransa REUTERS/Jacky Naegelen

Kakar masu yawan buda ido a kasar Fransa na gab da zama wacce zata fi karbar baki a wannan shekara ta 2015 a duniya, kamar yadda ofishin ma’aikatar harakokin wajen kasar ya sanar 

Talla

Ministan harakokin wajen kasar ta Fransa kuma mai kula da sha’anin yawan bude ido Laurent Fabius ya ce, baki masu yawan bude ido da zasu ziyarci Faransa a bana zasu kai miliyan 85, wanda ke nuna za a samu karin kashi  3.6% na abokan cinikayya daga kasashen ketare a kasar yayinda a lokaci guda masu ziyarar bude ido suka karu da kashi 2 cikin 100.

Sai dai ministan Harkokin wajen ya ce, an samu wannan ci gaba na masu ziyartar kasar ta Fransa ne bisa dalilai mabambanta da suka hada da na matsalolin tattalin arziki, ga kyawan yanayi da aka samu a kasar a yan watannin nan.

Har ila yau, tashe tashen hankullan da ake fuskanta a kasashe masu tasowa ya taimaka wajen kara yawan baki masu yawan buda ido, da ma faransawa dake zuwa ziyarar gida a faransa a daidai wannan lokaci cikin wannan shekara ta 2015.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.