UNESCO-Syria

UNESCO tace rushe giodan tarihin kasar Syria laifin yaki ne

Wani sashe a garin Palmyre na kasar Syria
Wani sashe a garin Palmyre na kasar Syria AFP PHOTO / JOSEPH EID

Hukumar Ilimi da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO, tace rusa daya daga cikin shahararun uraren tarihi dake birnin Palmyre na kasar Syriya, da kungiyar mujahidan Islama ta ISIS ta yi, daya ne daga cikin laifukan yaki da ya kamata wadanda suka aikata shi, su dandani hukumci abinda suka aikata.

Talla

A cikin wata sanarwa data fitar a yau litanin, babbar jami’ar hukumar raya ala’du ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, Uwargida Irina Bokova ta yi kiran kasashen duniya da su ci gaba da kasancewa a dunkule wajen yaki da lalata kayyakin tarihin duniya da ke ci gaba da faruwa a duniya

Mayakan na ISIS da suka mamaye birnin Palmyre tun cikin watan Mayun da ya gabata, a jiya lahadi ne suka daddasa nakiyoyi a gidan tarihin Baalshamin, inda suka ruguza kusan daukacin ginin, da tun a cikin karni na 17 aka ayyana shi a matsayin gado ga al’ummar duniya

A cewar hukumar ta UNESCO kusan daukacin cikin ginin ya rududduge, yayinda ginshikan dake kewaye da shi suka rushe
Bokova, ta kara da cewa a makon da ya gabata mayakan kungiyar ta ISIS suka fille kan tsoho shugaban gidan tarihin na Palmyre, Khaled al-Assaad, mai shekaru 82 a duniya, a yayinda rusa ginin da suka yi jiya ya kasance wani dadin laifin yaki da cin zarafin dan Adam da ISIS ta aikata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.