Jamus

Jamus ta sassauta dokar karbar ‘Yan gudun hijirar Syria

Mutanen Syria na ci gaba da kwarara zuwa Turai
Mutanen Syria na ci gaba da kwarara zuwa Turai REUTERS/Marko Djurica TPX IMAGES OF THE DAY

Kasar Jamus ta sassauta dokar karbar ‘Yan gudun hijira da ke neman mafaka daga kasar Syria a wani yunkuri na shawo kan matsalar kwararar baki ‘Yan ci-rani zuwa kasar.

Talla

Dubban mutanen Syria ne ke tsallako zuwa Hungaruy da Serbia da Macedonia domin shiga Jamus.

Jamus ta ce ta dai na mayar da ‘Yan gudunin hijirar na Syria zuwa kasar da suka fara isa a Turai. Lamarin da ya sa yanzu ta zama kasa ta farko da ta dai na yin korar bakin hauren.

Tarayyar Turai ta bayyana matsalar kwararan bakin haure a matsayin mafu muni, tun yakin duniya na biyu.

Ana sa ran a cikin wannan makon shugabanin Turai za su gudanar da taro domin samo hanyar magance matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI