Turai

Shugabannin Turai na son a mutunta Bakin-haure

Dubban 'Yan ci-rani ne da 'Yan gudun hijirar Syria ke kwarara Turai
Dubban 'Yan ci-rani ne da 'Yan gudun hijirar Syria ke kwarara Turai REUTERS/Bernadett Szabo TPX IMAGES OF THE DAY

Shgabannin Kasashen Turai sun bukaci al’ummar Nahiyar su mutunta bakin ‘Yan ci-rani da ‘Yan gudun hijira da ke kwarara zuwa nahiyar yayin da shugabannin ke shirin gudanar da wani taro na musamman kan yadda za’a shawo kan matsalar.

Talla

Kasar Luxembourg da ke shugabancin kungiyar tace ministocin cikin gida na Turai za su gudanar da taro ranar 14 ga watan Satumba domin bayar da shawara kan yadda gwamnatocin Yankin za su fuskanci matsalar.

Firaministan Italia Matteo Renzi yace lokaci ya yi da Turai za ta daina shirin daukar mataki don fuskantar matsalar kai tsaye.

Kiran taron ya biyo bayan bukatar haka da kasahsen Faransa da Birtaniya da Jamus suka yi.

Firaministan Faransa Manuel Valls ya ce ya zama dole a bar baki ‘yan kasashen waje da ke neman shiga kasar su shiga muddin sun fito inda ake cin zarafin su ko kuma kasar da ake yaki.

Valls da ke jawabi wajen taron jam’iyyar Socialists mai mulkin Faransa ya ce yana da kyau a dinga gagauta duba bukatar bakin dan daukar mataki akai.

Valls yace bakin dake tserewa kasashen su saboda yakin da ake tafkawa, ko kuma azabtar da su da ake yi ya zama wajibi a basu mafaka tare da mutunta su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI