Ukraine

Za a hukunta masu hannu a boren da aka yi a kasar Ukraine

Shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko
Shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko REUTERS/Valentyn Ogirenko

Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko yace za a hukunta dukkan wadanda ke da hannu wajen mummunan bore da aka yi jiya a harabar majalisar dokokin kasar dake birnin Kiev.

Talla

Cikin jawabin da yayi ga al’ummar kasar, shugaba Petro Poroshenko, yace boren da akayi ya sabawa dokokin kasar kuma za a sanya kafar wando daya da dukkan wadanda ke da hannu wajen kitsa boren ta aiwatar dashi.

Yayin wannan bore dai wani jami’in tsaro na kasar, mai kimanin shekaru 24 ya rasa ransa, sannan kuma wasu mutanen samada 100 suka sami raunuka.

Wannan bore na biyo bayan matakinda wakilan majalisar dokokin kasar suka dauka, na amincewa da wata doka dake bayar da kwara kwarar ‘yancin cin gashin kai, ga wasu yankuna na magoya bayan Gwamnati, amma kuma ‘yan tawaye ke rike dashi.

Shugabar harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini ta soki boren cikin wata sanarwa data fitar, inda take cewa abin takaici ne abin da ya faru.

Shugaban kasar Russia Vladmir Putin ta bakin wani ma’aikacinsa ya soki abinda ya faru, amma kuma ya kara da cewa harka ce ta cikin gidan kasar ta Ukraine.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.