Isa ga babban shafi
EU-Hungary

Ban Ki-moon ya soki Hungary saboda 'Yan gudun hijira

Sakatare Janar na MDD Ban Ki Moon.
Sakatare Janar na MDD Ban Ki Moon. REUTERS/Kim Hong-Ji
Minti 1

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya caccaki Kasar Hungary kan yadda Jami’an tsaronta suka ci zarafin ‘Yan gudun hijra a kan iyakar Kasar.

Talla

Mr. Ban ya ce ya damu matuka kan yadda jami’an tsaron suka wurga hayaki mai sa hawaye ga ‘Yan gudun hijirar dake kokarin tsallaka wa zuwa Kasar Serbia, al-amrin da ya ce ba za su amince da shi ba.

Hukumomin Hungary daik sun bayyabna cewa kimanin Jami’an tsaron 14 ne suka jikkata sakamakon tarzomar da ta barke tsakanisu da ‘Yan gudun hijirar a ranar laraba.

Wannan dai na zuwa ne bayan Shugabar gwamantin Jamus Angela Merkel ta bukaci Kungiyar Tarayyar Turai da ta shirya wani taro domin tattauna wa kan matsalar kwararar ‘Yan gudun hijirar da aka bayyana a matsayin mafi kamari tun bayan yakin duniya na biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.