Isa ga babban shafi
Faransa

Kotun Faransa ta bukaci a biya Ma'aikatan jirgi hakkinsu

Wasu jiragen Kasa na Faransa
Wasu jiragen Kasa na Faransa REUTERS/Charles Platiau
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Garba Aliyu
Minti 2

Wata kotun sasanta ma’aikata ta kasar Faransa ta zargi Hukumar kula da jiragen kasa ta kasar da laifin nuna kyama ga wasu ma’aikata 800 ‘yan kasar Morocco dake aikin jirgin kasa kuma ta bukaci a biya su hakki na Euro miliyan 150.

Talla

Wadannan rukunin ma’aikatan jiragen kasan tun shekara ta 1970 suke tare da kamfanin jiragen kasa na Faransa, kuma sun bayyana cewa sun kwashe shekaru mai yawa suna cikin halin kunci.

Su dai wadannan ‘yan kasar Morocco, hayansu a kayi daga kasar su a matsayin ‘yan kwangila masu zaman kansu, kuma aka hanasu matsayin ma’aikata na Faransa, ballantana su sami hakkin da ake baiwa ma’aikata bayan ajiye aiki.

Hatta wadanda suka zama ‘Yan kasar ta Faransa, kuma aka basu ayyukan na dindindin, sunyi kukan cewa an bata musu rayuwa.

Jimillan maaikatan jiragen kasan 832 suka gabatar da batun gaban kotun sasanta maaikatan kuma dukkaninsu zasu sami hakkinsu bayan sun kwashe shekaru masu yawa suna neman a basu.

Wadannan rukunin ma'aikata dai sun bayyana farin cikin su, game da wannan hukunci, amma kuma bangaren Hukumar jiragen kasan basu bayyana matakin gaba da zasu dauka ba.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.