Turai

Kotun Turai ta haramta wa fursunoni kada kuri'u

Kotun Turai ta bai wa kasashe damar haramta wa fursunoni kada kuri'u a lokacin gudanar da zabe a kasashensu.
Kotun Turai ta bai wa kasashe damar haramta wa fursunoni kada kuri'u a lokacin gudanar da zabe a kasashensu.

Babbar Kotun nahiyar Turai ta yanke hukuncin cewa kasashe na da damar haramta wa fursunonin da aka samu da aikata babban laifi, kada kuri’u a lokacin gudanar da zabe.

Talla

Wani Bafaranshe ne mai suna Thierry Delvigne ya daukaka kara zuwa kotun, bayan hukumomin Faransa sun haramta masa kada kuri’a a dukkanin zabubbukan kasar bayan an same shi da aikata babban laifi a shekara ta 1988.

To amma kotun wadda ke da cibiya a birnin Luxemburg, ta ce hukumcin haramcin kada kuri’un bai wuce gona da iri ba, domin kuwa kotun, ta yi la’akari da girman laifin da ya aikata, kuma ta bai wa sauran  kasashen damar haramta wa duk wani fursuna kada kuri'a matukar ya aikata babban laifi.

Manazarta da masu ruwa da tsaki a fannin tsaro, na sa ido kan wannan batun, inda Firaministan Birtaniya, David Cameron ya lashi takobin tabbatar da irin wannan haramcin kan duk wani fursuna dake kasar.

A bara dai, wata kotun kare hakkin dan adam ta Turai, ta yi tir da kasar Birtaniya da ta hana fursunoni yin zabe, inda ta kalli hakan a matsayin keta musu hakkin zabe.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.