Bosnia

Wasu Musulmin Bosnia na son a hukunta Kwamandojin MDD

Musulmin Bosnia na juyayin kisan kiyashi a Srebrenica
Musulmin Bosnia na juyayin kisan kiyashi a Srebrenica Reuters

Iyalan wasu Musulmin Bosnia uku da aka kashe lokacin da suke barin sansanin Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1995 sun bukaci kotun kare hakkin Bil Adama ta kasashen Turai da ta gurfanar da kwamandojin Majalisar guda 3 saboda sakacin da suka yi aka kashe su.

Talla

Matakin ya biyo bayan hukuncin wata kotun Holland da ta ki yarda a gurfanar da kwamnadojin guda uku.

Sojojin Serbia a karkashin jagorancin Ratko Mladic ne suka kashe Musulmin maza da yara kusan 8000, a shekarar 1995, kisan kiyashi mafi muni da aka bayyana tun kawo karshen yakin duniya na biyu.

Kwamandojin kasar Holland ne Musulmin na Bosnia ke son a hukunta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.