Austria

Austria za ta gina katanga saboda kwararar baki

'Yan gudun hijira a Nickelsdorf dake Autria
'Yan gudun hijira a Nickelsdorf dake Autria (©Reuters)

Kasar Austria ta bayyana shirinta na gina katanga a iyakarta da Slovenia domin maganace kwararar baki, matakin da ake ganin ya saba wa dokar Schengen ta kasashen Turai.

Talla

Tuni wannan matakin ya gamu da mummunar suka daga sauran kasashen Turai, inda kakakin gwamnatin Jamus Steffen Seibert ke cewa ba sa jin za a magance matsalar bakin da ake fuskanta ta hanyar gina katanga.

Kungiyar kasashen Turai ta ce ba a sanar da ita shirin ba, amma kuma shugabanta Jean claude Juncker zai gana da shugaban gwamanatin kasar Werner Faymann.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.