Faransa

Faransa ta ceto wasu baki da aka kulle a Mota

Baki da dama na ci gaba da kokarin shiga kasashen Turai ta ko wace hanya.
Baki da dama na ci gaba da kokarin shiga kasashen Turai ta ko wace hanya. AFP

Hukumomin Kasar Faransa sun ceto wasu baki 15 da aka kulle su a cikin bayan wata motar daukar kaya mai na’uarar sanyi. 

Talla

Jami’an tsaro sun ce daya daga cikin mutanen ne ya kira lambar kar ta kwana inda aka shiga binciken inda suke har aka gano motar da suke ciki amma babu direbanta.

To sai dai  a dai bayyana kasar da bakin suka fito ba.

A wani labari kuma kotu a Faransa ta bukaci hukumomin yankin Calais da su inganta wurin da aka ajiye bakin da suka shiga kasar ta Faransa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.