EU

Taron Turai da Afirka kan matsalar bakin haure

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai da Firaministan Malta Joseph Musca.
Shugaban Majalisar Tarayyar Turai da Firaministan Malta Joseph Musca. REUTERS/Darrin Zammit Lupi

Yanzu haka manyan jami’ai na kasashen Turai da kuma Afirka na gudanar da taro a kasar Malta inda suke tattaunawa kan matakan da suka dace domin tunkarar matsalar kwararar bakin haure zuwa cikin nahiyar Turai.

Talla

Babbar manufar taron dai ita ce samar da matakai domin tunkarar matsalar kwararar baki zuwa yankin.

A cewar shugaban sashen kula da bakin haure na hukumar tsaron yankin Turai Jean-Chrtistophe Dumont, ya ce lura yadda ake samun baki daga sassa daban daban na duniya da ke neman shiga yankin, dole ne a gayyace nahiyar Afirka.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.