Faransa

Faransa ta yi wa IS ruwan wuta a Syria

Faransa ta kai wa IS hare haren ramuwa bayan jerin haren haren Paris
Faransa ta kai wa IS hare haren ramuwa bayan jerin haren haren Paris AFP PHOTO / ECPAD

Jiragen Yakin Faransa sun kaddamar da munanan hare hare kan sansanin mayakan ISIS a Syria a wani mataki na ramako kan munanan hare haren da kungiyar ta dauki alhakin kai wa a Paris wanda ya lakume rayukan mutane 132.

Talla

Rahotanni sun ce jiragen yaki 12 suka kai jerin hare hare a Raqa inda suka jefa bama bamai 20 jim kadan bayan da shugaba Francois Hollande ya bayyana harin Paris a matsayin kaddamar da yaki tare da alkawarin daukar fansa.

Sama da mutane 350 suka samu rauni a hare haren da ‘Yan ta’adda suka kai a Paris .

‘Yan sandan Faransa sun bayyana sunan wani matashi Abdesalam Salah da suke nema ruwa a jallo wanda yana cikin mutane uku ‘yan uwan juna da ake zargi suna da hannu a hare haren Paris.

Kasashen Faransa da Amurka sun amince da shirin daukar kwararan matakan hadin kai domin murkuse mayakan kungiyar IS.

Ma’aikatan tsaron Amurka tace Sakataren tsaron kasar Ashton Carter da takwaransa na Faransa Jean Yves Le Drian suka amince da yarjejeniyar bayan hare haren Paris.

Peter Cook, mai Magana da yawun ma’aikatar tsaron yace ministocin biyu sun amince sojojojin su yi aiki tare wajen murkushe yan ta’adda musamman na kungiyar IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI