Faransa

Harin Paris: Ana neman Salah Abdeslam ruwa a jallo

Abdeslam Salah da 'Yan sanda Faransa ke nema ruwa a jallo kan harin Paris
Abdeslam Salah da 'Yan sanda Faransa ke nema ruwa a jallo kan harin Paris AFP PHOTO / POLICE NATIONALE

‘Yan sanda a Faransa na neman wani matashi mai suna Salah Abdeslam dan shekaru 26 da ake zargi tare da ‘Yan uwansa guda biyu suna da hannu a munanan hare haren da aka kai a Paris.

Talla

Tuni kasar Belgium ta bayar da sammacin kama shi, bayan kame dan uwansa Mohammed da ke kan hanyarsa zuwa Paris.

Ana zarginsu da hannu a hare haren da aka kai a Faransa bayan dan uwansu guda Brahimi ya kashe kansa a harin kunar bakin wake da ya kai a wani wurin cin abinci a birnin Paris.

‘Yan Sandan sun sanar da kame wata bakar motar da aka yi amfani da ita wajen kai hari gidan abinci a Montreuil da ke gabasin Paris.

Yanzu haka ‘Yan Sandan Faransa sun kama iyalan daya daga cikin ‘yan bindiga bakwai da suka kai mummunar harin da ya hallaka mutane 129 a birnin Paris.

‘Yan Sanda sun bayyana Omar Ismaila Mostefai a matsayin mahari na farko da aka gano ta hanyar yatsunsa da aka samu asasan jikin mutanen da suka mutu a gidan cashewa na Bataclan, inda aka hallaka mutane 89.

Jami’an ‘Yan Sandan sun tattara iyalan Mostefai su shida cikinsu har da mahaifinsa, inda yanzu haka ake musu tambayoyi.

Daga bisani ‘Yan Sandan sun sanar da gano mutumi na biyu daga cikin maharan da kuma wata mota shake da bindigogi kirar AK 47.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.