France

Air France ya karkata akalar jiragensa saboda fargaba

Jirgin Air France
Jirgin Air France REUTERS/Christian Hartmann/Files

Kamfanin jiragen sama na Air France ya sanar cewar, ya bada umurnin karkata akalar jiragensa guda biyu da suka tashi daga Amurka saboda barazanar sanya bam a cikin su.

Talla

Kamfanin ya ce, daya jirgin da ya tashi daga Los Angeles an karkata akalarsa zuwa birnin Salt Lake da ke Jihar Utah, yayin da na biyu da ya tashi daga Washington aka karkata shi zuwa Halifax a kasar Canada.

An dai gudanar da bincike kafin daga bisani jiragen su kara tashi zuwa Faransa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI