Harin Paris: 'Yan sanda sun cafke mutane uku
Wallafawa ranar:
Jami’an tsaron Faransa sun cafke mutane uku bayan sun kai samame a birnin Paris da nufin gano wadanda ake zargi da hannu a harin ranar juma’ar da ta gabata wanda ya yi sanadinyar mutuwar mutane 129 tare da jikkata 350.
Rohotanni sun ce mutane biyu sun mutu a samamen da ya hada da wata mata da ta tarwatsa kanta da bam, yayin da ake ta jin karar fashewar abubuwa da harbe harbe a tsakiyar birnin Saint-Denis da ke yankin Arewacin birnin Paris.
Akalalla jami’an ‘yan sanda uku aka raunata a binciken da suke yi game da harin wanda ya girgiza Faransa da kasashen duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu