Faransa

Wata mata ta tarwatsa kanta da bam a Faransa

'Yan sanda dake farautar 'yan ta'adda a Paris
'Yan sanda dake farautar 'yan ta'adda a Paris REUTERS/Christian Hartmann

Akalla mutane biyu suka mutu bayan ‘Yan sandan Faransa sun kaddamar da samame na tsawon sa’o’I bakwai a wani gidan da ake zargin na ‘Yan ta’adda ne da suka jagoranci munanan hare haren da aka kai birnin Paris a ranar Juma’a.

Talla

Wata mata ta tarwatsa kanta da bam yayin da kuma aka kashe daya daga cikin wadanda ake zargi ‘yan ta’adda ne a samamen da ‘Yan sandan Faransa suka kaddamar a unguwar Saint-Denis a Paris a yau Laraba.

An shafe tsawon sa’o’i bakwai ‘Yan sanda na barin wuta a wani gidan da ake tunanin na ‘yan ta’adda ne da suka jagoranci munanan hare hare 6 da a kai a Paris a ranar Juma’a.

‘Yan sandan sun kame mutane 7 a samamen sai dai babu tabbas a kan makomar wanda ake tunanin jagoransu ne Abdelhamid Abaaoud wanda Jami’an leken asirin Faransa suka ce yana cikin Paris

Wannan na zuwa ne a yayin da ‘Yan Majalisar Faransa ke shirin amincewa da bukatar shugaba Francois Hollande na tsawaita dokar ta-baci wanda zasu kada kuri’a a gobe Alhamis zuwa Juma’a.

Bayan kawo karshen samamen Hollande ya yabawa jami’an tsaron Faransa tare da neman goyon bayan kasashen duniya game yakin da kasar ta kaddamar akan maytakan IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.