Faransa

An gano Abdelhamid Abaaoud wanda ya kitsa harin birnin paris a mace

Hoton mayakin jihadi marigayi Abdelhamid Abaaoud  rike da kur'ani da kuma tutar musulunci
Hoton mayakin jihadi marigayi Abdelhamid Abaaoud rike da kur'ani da kuma tutar musulunci REUTERS

Wannan kuma na zuwa ne, bayan da masu bincike suka bayyana gano wasu alamun halitta a kan gawar mayakin jihadin, inda suka tabbatar da cewa gawar Abdelhamid Abaaoud, da aka kashe a lokacin wani samame da jami’an yan sanda 110 suka kai a maboyarsa inda aka samu wata mata yar kunar bakin wake da ta kanta da Bam a jiya Laraba cewar mai shigar da karar kasar ta Faransa François Molins.  

Talla

Mai shigar da karar ya kara da cewa an gudanar da binciken ne gano mayakin ne a wata gawa da aka gano a ginin, dake dauke da almun harbin harsashen bindiga, kamar yadda masu kula da bincike kan harin ta’addanci mafi muni da aka taba kaiwa a tarihin kasar Faransa, da kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane 129 tare da jikkata wasu 350 a ranar juma’ar da ta gabata a birnin Paris.

A cikin gaggawa PM Faransa Manuel Valls ya yaba kan nasarar da yan sanda suka samu wajen murkushe yan ta’addan.

A gaban yan majalisar dokokin kasar Mr Valls ya ce Abaaoud, ne kwakwalwar da ya shirya kai wannan hari, sai dai kuma ya bukaci yin taka tsantsan duk da cewa sun san wanda ake kallo a matsayin barazana na daga cikin mamatan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.