TARAYYAR TURAI-BAKIN-HAURE

Dokar tattance bakin haure dake shiga Turai

Wasu daga cikin 'Yan gudun hijira
Wasu daga cikin 'Yan gudun hijira RFI/Laurent Geslin

Kasashen yankin Balkan sun soma aiwatar da sabbin matakai domin hana shigar ‘yan gudun hijirar Syria zuwa yankin, inda daga yanzu sai an tabbatar da cewa masu gujewa yaki ne kawai za su iya tsallaka iyakokinsu.

Talla

Matakan dake zuwa a lokacin da Faransa ta gabatar wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Dimkin Duniya  da wani daftarin kuduri, wanda zai bai wa kasashen duniyar damar yin amfani da dukkanin matakan da suka ganin cewa sun wajaba domin kawo karshen kungiyar ISIS.

Daftarin wanda Faransa ta gabatar a yammacin jiya Alhamis, ya bukaci kasashen Duniya da su hada gwiwa domin yaki da kungiyar da kuma sauren kungiyoyi na ‘yan ta’adda cikin su kuwa har da Alqa’ida.

Sakamakon fara aiki da wadannan sabbin matakai, yanzu haka dubban ‘yan gudun hijira ne suka makalle akan iyakar kasar Girka da Macedonia.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.