Faransa

Faransa ta bukaci EU ta rage yawan baki

Firaministan Faransa  Manuel Valls
Firaministan Faransa Manuel Valls REUTERS/Charles Platiau

Firaministan Faransa Manuel Valls ya bukaci kungiyar kasashen Turai, EU ta rage yawan bakin da ke kwarara yankin sakamakon barazanar tsaron da ake fuskanta bayan kazamin harin da aka kai birnin Paris. 

Talla

Valls ya ce lokaci yayi da Turai za ta ce ba za ta ci gaba da karbar baki ba ganin irin halin da yankin ya samu kansa.

Kungiyar kasashen Turai ta amince ta aiwatar da sauye sauye kan amfani da fasfo na Schengen da ake amfani da shi a wasu kasashensu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI