Isa ga babban shafi
Faransa

An rufe Masallatai 3 a Faransa

Ministan cikin gidan Faransa Bernard Cazeneuve yayin baiwa 'Yan sanda kasar umarni
Ministan cikin gidan Faransa Bernard Cazeneuve yayin baiwa 'Yan sanda kasar umarni Reuters/路透社
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
1 Minti

‘Yan sanda a Faransa sun cafke Musulmi sama da 230 tare da rufe masallatai 3, Sakamakon dokokin dokar ta bacci da aka sanya a birnin Paris makon daya gabata bayan harin da aka kai Kasar.

Talla

Ministan harkokin cikin gidan Faransa Bernard Cazeneuve ya ce ‘yan sanda kasar sun kai samame ne kan masallatan dake gashin birnin kasar a safiyar yau, inda cikin mutane 232 da suka cafke, akayi wa mutane 9 daurin talala tare da haramtawa wasu 22 barin kasar

Cazeneuve ya kuma bayyana cewa daga lokacin da aka kai harin birnin Paris zuwa yanzu ‘yan sanda sun kai samame a sassa dubu 2,235 a fadin kasar, inda sukayi nasara kwace makamai 334.

Tun lokacin da Faransa ta kafa dokar ta bacci tare da karawa Jami’an tsaron ta karfi, ake samun korafin daga wasu al’ummar kasar, dama kungiyoyin fararan hula da wasu’ yan siyasa dake bayyana damuwarsu kan yadda ‘yan sanda kasar ke amfani da wannan dama wajen muzguna mutane.

Korafin da Cazeneuve ya yi watsi da ita, inda yake cewa ya zama dole su dau wanann matakai domin murkushe ayyukan ta’ddanci a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.