Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande ya ziyarci Masallacin Paris

Shugaban Faransa Francios Hollande, da Firaminista Manuel Valls sun jagoranci gangamin tuna harin da aka kai wa Mujallar charlie a Paris
Shugaban Faransa Francios Hollande, da Firaminista Manuel Valls sun jagoranci gangamin tuna harin da aka kai wa Mujallar charlie a Paris REUTERS/Philippe Wojazer
Zubin rubutu: Abubakar Issa Dandago
Minti 2

Shugaban Kasar Faransa Francois Hollande ya kai ziyarar ba-zata babban Masallachin birnin Paris a dai dai lokacin da ake cika shekara guda da harin da aka kai wa Mujallar Charlie Hebdo da ke zanen barkwanci.

Talla

Rahotanni sun ce shugaba Hollande ya kai ziyarar ne ta ba-zata da ranar Lahadi inda ya zauna ya sha shayi da Musulman da ke ciki sannan ya tattauna da su.

Fadar shugaban kasar tace shugaban ya je Masallacin ne bayan ya halarci wani karamin taro domin tuna irinsa da aka yi shekara guda da ta wuce wanda ya samu halartar mutane sama da miliyan daya da rabi da kuma shugabanin kasashe da dama.

Rahotanni sun ce Masallatan da ke kasar Faransa sun bude kofofinsu ga jama’a don ganin a dinke barakar da aka samu sakamakon hare-haren da aka kai kasar da kuma niyyar fahimtar addinin Islama.

Rahotanni sun ce Musulmi da dama sun fuskanci tsangwama a Faransa sakamakon hare-haren da aka kai kasar da ke da nasaba da ayyukan ta’adanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.