Isa ga babban shafi
Faransa-India

Francois Hollande na ziyarar aiki a kasar India

Francois Hollande da Nerendra Modi a ranar 24-01-2016
Francois Hollande da Nerendra Modi a ranar 24-01-2016
Zubin rubutu: Abdoulkarim Ibrahim
Minti 1

Shugaban Faransa Francois Hollande ya isa kasar India domin gudanar da zaiyarar aiki ta yini uku a kasar, inda a yau ya fara da birnin Chandigard kafin daga bisani ya wuce zuwa New Delhi a gobe litinin.

Talla

Batun kasuwanci da kuma hulda a fagen aikin soji, na daga cikin abubuwan da shugaba Hollande zai tattauna da Firaministan India Nerandra Modi.

A lokacin da ya kai ziyara a Faransa cikin shekarar da ta gabata, Firaminista Modi, ya ce India za ta sayo jiragen yaki guda 36 daga Faransa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.