Turai

Turai ta fitar da sunayen mutanen da ta ke nema

'Yan sandan Turai na neman maharan Paris ruwa a jallo
'Yan sandan Turai na neman maharan Paris ruwa a jallo Reuters
Minti 1

Kasashen Turai sun fitar da jerin sunayen mutanen da suke nema ruwa a jallo da suka hada da mayakan kungiyar ISIS da ake zargi da kaddamar da hari a birnin Paris na kasar Faransa, inda mutane 130 suka rasa rayukansu a bara.

Talla

A jiya jumma’ ne hukumomin jami’an ‘yan sandan Turai suka sanya jerin sunayen mutane 45 a shafin internet, a wani mataki na kara yada bayanai game da wadanda ake zargi da hannu a harin Paris

Bayanan dai na dauke da hotunan mutanen da kuma kwatancen yanayinsu har ma da irin ta’adin da suka aikata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.