WHO-ZIKA

Kamfanin Sanofi a Faransa ya soma binciken Riga kafin Zika

Sauron dake yada zazzabin Zika
Sauron dake yada zazzabin Zika RFI

Wani kamfanin harhada magunguna a kasar Faransa mai suna SANOFI, ya sanar da soma binciken hada maganin kwayar cutar Zika, dake sa ana haifar yara da matsalar kwakwalwa.

Talla

A cewar wannan kamfani, da zarar sun kamala binciken zasu futo da maganin da zai zama maganin kwayar cutar ta Zika da yanzu ke cigaba da yaduwa tamkar wutar daji a kasashen latin Amurka da Turai.

Bugu da kari kamfanin ya ce za’a samu mafita ga wannan annoba, ta hanyar dakile yaduwarta.

Wannan sanarwa dai na zuwa ne kwana guda bayan da hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta bayyan cutar a matsayin wata annoba ga Duniya.

Kawo yanzu babu maganin cutar da ke haddasa haifar yara da matsalar kwakwalwa, bayaga sauya halittun su, ta hanyar haddasa haifar su da kananan kawuna.

Amma sai dai kamfanin na SANOFI yace akwai nasara ga wannan bincike da yake akan samar da maganin na zazzabin Zika.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.