Faransa

Kotun Faransa na tuhumar tsohon jami’in Sarkozy

Claude Guéant daya daga cikin jami'an gwamnatin Nicolas Sarkozy
Claude Guéant daya daga cikin jami'an gwamnatin Nicolas Sarkozy AFP PHOTO / KENZO TRIBOUILLARD

Kotu a Faransa na tuhumar daya daga cikin manyan na hannun damar tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy Claude Gueant da taimakawa wajen canza alkaluman wata kur’iar raba gardama domin nuna kwarjinin tsohon shugaban.

Talla

Claude Gueant, tsohon sakatare ne a fadar shugaba Sarkozy, kuam a cikin watan Nuwambar da ya gabata, wata kotu ta yanke masa hukuncin daurin talala na tsawon shekaru biyu, tare da hana shi rike mukamin gwamnati a cikin shekaru biyar masu zuwa, sakamakon samun shi da laifin zuba wa ma’aikatar cikin gidan kasar wasu kudade alhali yana rike da mukami a fadar shugaban kasar.

Har ila yau wata kotun na zargin Gueant da kaucewa biyan haraji, yayin da a daya gefen ake zarginsa da hannu wajen karbo makudden kudade daga tsohon shugaban Libya Mu’ammar Kaddafi don gudanar da yakin neman zaben Sarkozy a shekata ta 2007.

Manazarta al’amurran siyasar kasar ta Faransa dai na ganin cewa, zarge-zargen da ake yi wa magoya bayan Sarkozy, za su iya yin mummunan tasiri ga yunkurinsa na tsayawa takarar neman shugabancin kasar a shekara mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.