Slovakia

Fira Ministan Slovakia ya Gaza Samun Gagarumin Rinjaye Bayan Zaben Majalisa

Fira Ministan kasar Slovakia Robert Foco ya lashe zaben wakilan majalisar Dokokin kasar da aka gudanar amma kuma jamiyyun adawa za su dama lissafi wajen kafa sabuwar Gwamnati. 

Fira Ministan Slovakia Robert Fico
Fira Ministan Slovakia Robert Fico SAMUEL KUBANI / AFP
Talla

Robert Fico mai hakidar kyamar baki, kamar kawayen kasar sa Poland da Hungary ya sami kashi 28.3 daga cikin dari na kuriu da aka jefa nesa da sauran, amma kuma bai sami kashi 35 daga cikin dari ba kamar yadda wasu kafofin yada labarai suka yi ta hasashe.

Kasar Slovakia ake sa ran ta shugabancin kungiyar Tarayyar Turai a tsarin karba-karba na shugabancin kungiyar daga watan bakwai na wannan shekara.

Yanzu ya rage wa Fira Ministan kafa Gwamnatin hadaka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI